![]() |
| Manyan Batutuwan Arewa da Siyasa Ta Ɗauke Mana Hankali a Kai |
Canja jam’iyyar Abba ya ɗauke hankalinmu daga manyan matsalolin da suka shafi rayuwar al’ummar Arewa baki ɗaya. Duk da hayaniyar siyasa, akwai muhimman batutuwa na tsaro, adalci da mutuncin ɗan Adam da bai kamata mu yi shiru a kansu ba. Wajibi ne mu ci gaba da tunatar da kanmu da shugabanni game da waɗannan lamurra kamar haka:
1. Lamarin jami’in DSS da ya sace ’yar Jigawa ya kuma canja mata addini
Wannan lamari babban cin zarafi ne ga doka, addini da haƙƙin ɗan Adam. Idan jami’in tsaro da aka ba amanar kare rayuka da ’yanci shi ne zai yi amfani da mukaminsa wajen aikata irin wannan laifi, to al’umma na cikin hatsari. Ba za a yarda a nuna bambanci ba; wajibi ne a bincike shi a fili, a gurfanar da shi gaban kuliya, sannan a hukunta shi daidai gwargwado, kamar yadda aka yi wa Yunusa Yalo. Adalci dole ya zama ɗaya ga kowa, ba tare da la’akari da mukami ko ƙarfi ba.
2. Kisan gilla da aka yi wa iyalan Mal. Haruna
Abin takaici ne yadda muka yi shiru kan wannan lamari mai zafi wanda ya shafi zubar da jinin fararen hula. Rayuwar ’yan Arewa ba ta da rahusa, kuma bai kamata mu bari irin wannan kisan ya ɓace a cikin labarai ba. Dole ne mu ci gaba da matsa lamba har sai an kammala cikakken bincike, an gano waɗanda suka aikata laifin, kuma an hukunta su. Wannan ne kaɗai zai rage tashin hankali da kuma dawo da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro.
3. Maganar Chairman INEC, Amupitan, game da kisan Kiristoci
Idan har shugaban INEC ya rubuta wa wata ƙasa cewa ana kisan kiyashi wa Kiristoci a Najeriya, to wannan magana tana da nauyi sosai kuma tana iya ɓata sunan ƙasa da kuma haifar da rikici. Idan yana da hujjoji, wajibi ne ya gabatar da su a cikin gida, ta hanyoyin da doka ta tanada. Idan kuma magana ce ta son zuciya ko siyasa, to bai dace ya ci gaba da rike wannan mukami ba. Saboda haka, wajibi ne ya yi murabus ko kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi domin kare mutuncin ƙasa da zaman lafiya.

0 Comments